Sojoji sun kashe yan bindiga biyu a Plateau

Dakarun  sojan Najeriya dake karkashin rundunar samar da tsaro a jihar  Plateau ta Operation Safe Haven sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin yan bindiga ne a kusa da garin   Nemaledu dake karamar hukumar Wase ta jihar.

A tabakin mai magana da yawun rundunar, Major Samson Zhakom dakarun sun kai farmakin ne biyo bayan gamsassun bayanan sirri da suka cewa anga motsin yan ta’adda a yankin.

Ya ce sojoji daga shiya ta 3 na rundunar ne suka yi kwanton bauna kusa da maboyar batagarin inda suka fafata da su a arangamar da suka yi.

Ya kara da cewa dakarun sun samu nasarar kwato bindiga AK-47 guda daya kirar gida.

Zhakom ya bayyana muhimmancin  bukatar dake akwai ta hadin kan al’umma ga jami’an tsaro inda ya ce hakan zai hana batagarin samun maboya a yankin.

More from this stream

Recomended