Sojoji sun kashe Tahir Baga kwamanda a ƙungiyar Boko Haram Tahir Baga

Dakarun  sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai sun samu nasarar kashe, Tahir  Baga wani jigo kuma kwamanda a ƙungiyar Boko Haram a cigaba da farmakin da suke kaiwa maɓoya yan ta’addar dake Dajin Sambisa.

An kashe Tahir ne a ranar 13 ga watan Mayu na shekarar 2024 a wani gagarumin farmaki da aka yiwa laƙabi  da Operation Desert Sanity III  domin kakkabe ƴan ta’addar daga Shababul Umma, Garin Panel Beater da Lagara Anguwan Gwaigwai dake tsakiyar dajin na Sambisa.

Wasu majiyoyin jami’an tsaron sirri sun faɗawa Zagazola Makama dake wallafa bayanai a kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa  a lokacin  farmaki dakarun sojan sun yi arangama da ƴan ta’addar inda suka yi musu ɓarin wuta har ta kai ga sun kashe Baga da kuma wasu mabiyansa a yayin da wasunsu da dama suka tsere da raunin harbin bindiga.

Tahir Baga ya kasance makusanci ga tsohon shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau kuma yana ɗaya daga cikin mutanen farko da suka kafa kungiyar ta Boko Haram a birnin Maiduguri kafin su koma Dajin Sambisa tare da su Mamman Nur, Khalid Albarnawi, Abubakar Shekau, Kaka Ali, Mustapha Chadi, Abu Maryam da Abu Krimima.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...