
Dakarun rundunar sojan Najeriya dake karkashin rundunar samar da tsaro ta Operation Hadin Kai dake aiki a yankin arewa maso gabas sun dakile wani hari da mayakan kungiyar yan ta’adda ta ISWAP suka kai a garin Damboa dake jihar Borno.
Dakarun sojan sun samu dauki ta sama daga jiragen yakin rundunar sojan saman Najeriya a gwabzawar da bangarorin biyu suka dauki tsawon sama da sa’o’i biyu a nayi.
A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Juma’a rundunar ta ce da misalin karfe 1 na daren ranar 23 ga watan Mayu ne sojojin sun hangi yan ta’addar a Damboa inda suka gaggauta bude musu wuta.
Sanarwar ta ce akalla yan ta’adda 16 aka kashe a gwabzawar da aka yi.
Yan ta’addar sun hari wani sansanin soja ne dake garin amma dakarun sojan dake wurin suka tilastawa musu tserewa da kafafunsu sakamakon asarar rayukan da suka yi.
Sanarwar ta kara da cewa duk da cewa an dakile harin makamin roka da yan ta’addar suka harba ya tayar da gobara a wani gini da ake ajiye harsashi amma an ci nasarar shawon kan wutar.