Ɓangaren sojan sama na rundunar Operation Haɗin Kai sun kashe mayaƙan ƙungiyar ISWAP sama da 70 a wani farmaki da suka kai musu a kudancin yankin tafkin Chadi.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi jiragen yaƙi sun harba makami mai linzami ranar 5 ga watan Nuwamba kan sansanonin gawurtaccen ɗan ta’adda, Usman Russia.
Makama ya rawaito cewa makamin da aka harba ya sauka kan sansanonin Kwallaram da Arainna Ciki dake kusa da Jibillaram a ƙaramar hukumar Marte ta jihar Borno.
Rahoton ya ce ƴan ta’adda 79 aka tabbatar da an kashe a sansanin Kwallaram.
Yawan ƴan ta’adda da aka kashe a sansanin Arainna Ciki na da yawan gaske duk da cewa ba a tabbatar da yawansu ba sakamakon irin yanayin munin harin da aka kai musu.