Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar wuta a sansanin mayaƙan kungiyar dake Ejemekuro a ƙaramar hukumar Oguta ta jihar Imo.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojan Najeriya, Onyeama Nwachukwu ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Nwachukwu ya ce sojojin sun murƙushe turjiyar da ƴan tada ƙayar bayan suka nuna sakamakon manyan bindigogi da sojin suke da su har ta kai ga sun samu nasarar kwato tarin makamai da dama.

A cewarsa bindigogin da aka gano sun haɗa da AK-47 guda ɗaya, bindigogi ƙirar Pump Action guda biyu, bindiga guda ɗaya ƙirar gida, gidan harsashi guda biyu da kuma harsashi guda uku..

Ya ce sojojin sun kuma gano baburan hawa guda biyu, wayoyin hannu biyu da kuma hular kakin soja koriya.

More from this stream

Recomended