Sojoji sun kashe gawurtaccen dan bindiga a jihar Sokoto

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta dake aiki a Rundunar Operation Fansar Yamma sun samu nasarar kashe gawurtaccen dan bindiga da ake kira da Dan Dari Biyar a lokacin da su ke aikin kakkabe yan bindiga a yankin yammacin karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

A cewar Zagazola Makama masani kan yaki da yan ta’adda majiyoyin jami’an tsaro sun bayyana cewa an kashe dan bindigar ne a ranar Alhamis lokacin da yake kokarin karbar kudin fansa daga wasu yan uwan wadanda ya yi garkuwa da su a wani daji dake tsakanin kauyukan Turtsawa, Mazau da Zango.

Majiyoyin na tsaro sun fada masa cewa farmakin wani bangare ne na zafafa hare-hare sojoji dan kakkabe yan bindigar daga wuraren da suka yi karfi.

An kai farmakin ne a wani hadin gwiwa da dakarun soja da kuma jami’an tsaro na sa kai dake aiki karkashin shirin samar da tsaro na gwamnatin jihar Sokoto.

Makamai da kuma kayayyakin sadarwa aka samu nasarar ganowa a wurin da aka yi musayar wutar.

More from this stream

Recomended