Sojoji sun kashe BH biyu tare da ceto wasu mata 6 da yara 10

A kokarin da rundunar sojan Najeriya take na kakkabe yan ta’adda a yankin arewa maso.Sojoji tare da taimakon jami’an tsaron sa kai na Civilian JTF sun gudanar da aikin kakkabe yan ta’adda a yankin da Agapaluwa dake jihar Borno.

Zaratan sojojin sun yi arba da yan ta’addar inda suka samu nasarar kashe biyu daga ciki.

A wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce sojojin sun kuma samu nasarar ceto wasu mata 6 da kuma yara goma wadanda yan ta’addar ke tsare da su.

Har ila yau rundunar ta samu nasarar gano wasu kayayyakin amfanin gona da yan BH suka sace inda kuma aka kona su nan take a wurin.

Ga wasu daga cikin hotunan abinda ya faru:

More from this stream

Recomended