Akalla ‘yan ta’adda 28 ne aka kashe yayin da sojoji suka kama wasu 114 a wani samame a fadin kasar tsakanin 7 da 17 ga Agusta, 2023.
Hedikwatar tsaron ta ce wadanda aka kama sun hada da ‘yan ta’adda 92, ‘yan bindiga shida, masu garkuwa da mutane uku, masu hadin gwiwa da ƴan ta’addar shida, da kuma wadanda ake zargin barayin mai ne guda bakwai.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan ayyukan sojojin da suka yi a lokacin da ake nazari a Abuja.
Buba ya kuma ce an ceto fararen hula 82 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce, “Jami’an sojoji maza da mata za su ci gaba da sanya kansu da karfinsu don kare al’ummarmu mai daraja.”