![](https://arewa.ng/storage/image_editor_output_image-303582473-17179660395177470967538550868178-1024x843.jpg)
Dakarun rundunar Operation Whirl Punch dake aikin samar da tsaro a jihar Kaduna sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin ƴan fashin daji ne.
A wata sanarwa ranar Litinin, Samuel Aruwan kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya ce an tare waɗanda ake zargin ne a ƙaramar hukumar Kajuru dake jihar.
Aruwan ya ce sojojin sun ƙwace bindigar AK-47 guda biyu, bindigar mashin gan ƙirar gida, gidan zuba harsashin AK-47 guda 9, har sashi 250, babura guda biyu sai kuma rediyo guda biyu.
Sanarwar ta ce sojojin sun yi arangama da ƴan bindigar a ƙauyen Ɗantarau nan take aka kashe biyar daga cikinsu bayan musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ƴan bindigar sun tsere da raunin harbin bindiga inda ya shawarci jama’ar yankin da suka idanu sosai kuma kada su sake su taimakawa ƴan bindigar da ka iya zuwa neman magani.
Tuni gwamnan jihar Mallam Uba Sani ya yabawa jami’an tsaron kan ƙoƙarinsu na inganta tsaro a jihar.