
Dakarun sojan Najeriya na rundunar samar da tsaro ta Operation Fansan Yamma sun samu nasarar kashe wasu ƴan fashin daji hudu tare da kama guda ɗaya a wani farmaki dare da suka kai a ƙauyen Nasarawa dake ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Wasu majiyoyin jami’an tsaron sirri sun faɗawa Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro cewa an kai farmakin ne da tsakar daren ranar 10 ga watan Fabrairu har ya zuwa asubahin washegarin ranar.
A cikin waɗanda aka kashe akwai wani mutum guda daga ƙauyen na Nasarawa da aka daɗe ana zargin yana da alaƙa da aikata miyagun laifuka a yankin.