Sojoji Sun Kashe Ɗan Fashi, Sun Ceto Wanda Aka Sace a Jihar Filato

Dakarun Runduna ta 3 da ke ƙarƙashin Operation Safe Haven, waɗanda ke aiwatar da aikin tsaro na Operation Lafiyan Jama’a, sun kashe ɗan fashi guda tare da ceto wani da aka sace a yankin ƙaramar hukumar Wase da ke Jihar Filato.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Nantip Zhakom, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa samamen ya biyo bayan samun sahihin bayanan sirri ne dangane da motsin wasu ƴan fashi da suka yi garkuwa da wani mazaunin yankin.

A cewarsa, dakarun sun kakkabe ƴan fashin ne a wajen da suka saba ketarewa da babur, inda suka ci karo da su yayin da suke jigilar wanda suka sace. An kashe ɗaya daga cikin ƴan fashin, yayin da sauran suka arce cikin daji, suka bar wanda suka kama.

An gano cewa wanda aka ceto ɗin shi ne Mista Adamu Alhaji Nuhu, ɗan shekara 45. Haka kuma dakarun sun kwato bindiga ƙirƙira guda ɗaya, magazin ɗin bindiga, harsasai huɗu masu girman 9mm, babur nau’in Boxer, da wasu kayayyaki da ƴan fashin suka bari.

Sanarwar ta ƙara da cewa, dakarun na riƙe da kayayyakin da aka kwato domin ci gaba da bincike.

A halin yanzu, sojojin na ci gaba da aikin bincike da sintiri don kamo sauran ƴan fashin da suka gudu.

More from this stream

Recomended