Sojoji sun kashe ɗan bindiga a Kaduna

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun kashe yan bindiga da kuma gano bindigar AK-47 ɗaya a Kaduna.

Jami’an sojojin rundunar shiya ta ɗaya ne suka kai farmakin a kananan hukumomin Chikun da Kajuru.

Musa Yahaya mai rikon muƙamin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojan Najeriya shiya ta ɗaya shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

Ya ce sojojin bisa dogaro da bayanan sirri sun yi kwanton ɓauna a kan hanyar da ƴan bindigar suke bi a titin Kwant-Kabai-Kubusu a ranar Laraba.

Yahaya ya ce farmakin wani bangare ne na ƙoƙarin da rundunar take na raba jihar da ƴan ta’ada, ƴan bindiga da kuma sauran batagari dake dazukan jihar.

Ya ce a yayin farmakin a musayar wutar da aka yi ɗan bindiga guda ya rasa ransa yayin da sauran suka tsere da raunin harbin bindiga.

“bindigar AK-47 guda ɗaya, gidan harsashi ɗaya, maganin dabbobi da kuma kayan sawa su ne aka gano” a cewar sanarwar.

More from this stream

Recomended