Sojoji sun kashe ƴan ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta’adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno.

A wata sanarwa ranar Asabar rundunar sojan ta ce an kashe ƴan ta’addar ne a ranar 19 ga watan Afrilu.

Rundunar sojan ta ce dakarunta sun yi arangama da ƴan ta’addar a wajejen ƙauyen Nguma ta kara da cewa an gano babur ɗaya da kekuna 6 sai bindiga ƙirar AK-47 da kuma sauran kayayyaki da aka yi watsi da su.

A kuma wani samamen na daban dakarun sojan na Najeriya sun kai samame a ƙauyen Abuni dake ƙaramar hukumar Awe ta jihar Nasarawa kan wasu maɓoyar bata gari inda aka gano bindigogi.

An samu nasarar gano bindigogi biyu ƙirar AK-47 a gidan wani da ake kira Abdullahi Musa tare da kama ƙarin wasu mutane.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...