Sojoji sun kashe Æ´an fashin daji 5 a Kaduna

Dakarun rundunar Operation Whirl Punch dake aikin samar  da tsaro a jihar Kaduna sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin ƴan fashin daji ne.

A wata sanarwa ranar Litinin, Samuel Aruwan kwamishinan  tsaro da harkokin cikin gida ya ce an tare waɗanda  ake zargin ne a ƙaramar hukumar Kajuru dake jihar.

Aruwan ya ce sojojin sun ƙwace bindigar AK-47 guda biyu, bindigar mashin gan ƙirar gida, gidan zuba harsashin AK-47 guda 9, har sashi 250, babura guda biyu sai kuma rediyo guda biyu.

Sanarwar ta ce sojojin sun yi arangama da Æ´an bindigar a Æ™auyen ÆŠantarau nan take aka kashe biyar daga cikinsu bayan musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro.

Ya Æ™ara da cewa wasu daga cikin Æ´an bindigar sun tsere da raunin harbin bindiga inda ya shawarci jama’ar yankin da suka idanu sosai kuma kada su sake su taimakawa Æ´an bindigar da ka iya zuwa neman magani.

Tuni gwamnan jihar Mallam Uba Sani ya yabawa jami’an tsaron kan Æ™oÆ™arinsu na inganta tsaro a jihar.

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa É—ansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...