Sojoji sun kashe ƴan fashin daji 5 a Kaduna

Dakarun rundunar Operation Whirl Punch dake aikin samar  da tsaro a jihar Kaduna sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin ƴan fashin daji ne.

A wata sanarwa ranar Litinin, Samuel Aruwan kwamishinan  tsaro da harkokin cikin gida ya ce an tare waɗanda  ake zargin ne a ƙaramar hukumar Kajuru dake jihar.

Aruwan ya ce sojojin sun ƙwace bindigar AK-47 guda biyu, bindigar mashin gan ƙirar gida, gidan zuba harsashin AK-47 guda 9, har sashi 250, babura guda biyu sai kuma rediyo guda biyu.

Sanarwar ta ce sojojin sun yi arangama da ƴan bindigar a ƙauyen Ɗantarau nan take aka kashe biyar daga cikinsu bayan musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ƴan bindigar sun tsere da raunin harbin bindiga inda ya shawarci jama’ar yankin da suka idanu sosai kuma kada su sake su taimakawa ƴan bindigar da ka iya zuwa neman magani.

Tuni gwamnan jihar Mallam Uba Sani ya yabawa jami’an tsaron kan ƙoƙarinsu na inganta tsaro a jihar.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...