Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe ƴan bindiga 6 lokacin da suke sintiri a yankin ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a jihar Kaduna.
Samuel Aruwan kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida shi ne ya bayyana haka inda ya ce sojojin sun samu makamai da harsashi da suka haɗa da bindigar AK-47 guda biyu gidan harshi guda 4, yunifam ɗin yan ta’addar na mutum 40 da kuma baburan hawa 9.
Sanarwar ta ce sojojin sun yi arangama da ƴan bindigar ne a yankin Mindaro, Kidandan da kuma Ngade.
Aruwan ya ce gwamnan jihar, Uba Sani ya ya yaba tare da jin ɗaɗin labarin kisan yan bindigar.