Sojoji sun kama wasu ɓatagari biyar ɗauke da bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar tsaro ta Operation Safe Haven dake aikin samar da tsaro a jihar Filato da kuma wani sashe na jihar Kaduna sun kama wasu mutane biyar da tare da ƙwace bindigogi a lokuta daban-daban a ƙaramar hukumar Jos south ta jihar Filato.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya bayyana cewa cikin wadanda aka kama akwai wani mai suna Stephen Maisaje ɗan shekara 28 da ake zarginsa da Safar bindiga.

An kama Maisaje ranar 17 ga watan Nuwamba  da misalin ƙarfe 08:30 na dare a wani shingen binciken ababen hawa dake Kwanan Fulani a jihar biyo bayan ƙwararan bayanan sirri da jami’an tsaron suka samu.

A yayin binciken ne aka gano bindiga ƙirar AK-47 ƙirar gida da harsashi guda 15 wuƙa da kuma babur na hawa.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa zai yi safarar bindigar ne ya zuwa yankin Farar Lamba dake Jos south.

A wani binciken na daban sojoji sun samu nasarar kama karin wasu mutane huɗu a wani shingen binciken na daban sa’o’i biyu bayan kama Maisaje duka  yankin .

Waɗanda aka kama sun haɗa da Benjamin Mwanta, shekaru 26; Bitrus David, mai shekaru 38; Joseph Davou,mai shekaru 27; da kuma  Christopher Jah, mai shekaru 26.

Kayan da aka gano a wurinsu sun haɗa da bindigogi biyu ƙirar AK-47 ɗaya ƙirar gida harsashi guda ɗaya, wukar sojoji, wayoyi guda huɗu sai babur guda uku.

More from this stream

Recomended