Sojoji sun kama wani hatsabibin barawo mai garkuwa da mutane a jihar Zamfara

[ad_1]
Sojojin Najeriya da suka fito daga Rundunar Sojan Najeriya Shiya ta Daya, sun kashe wasu barayi biyar ciki har da kasurgumin barawon nan da ake kira da Sani Danbuzuwa da ya fito daga jihar Zamfara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a Kaduna mai dauke da sahannun jami’in hulda hulda da jama’a na shiryar, Kanal Muhammad Dole.

Ya ce soja daya ya mutu lokacin da suka rufafa yan fashin ya zuwa cikin dajin Kwuyambana dake jihar Zamfara ya yin da wasu biyu kuma suka jikkata ya kara da cewa “Wadanda suka jikkata an dauke su ya zuwa asibitin asibitin sojoji sojojin dake Kaduna kuma suna murmurewa.”

“Sojojin sun amsa kiran kai daukin gaggawa akan ana aikata fashi da makami akan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua inda wasu da ake zargin barayin ne sukai musu kwanton bauna.

“Amma sun samu nasarar fin ƙarfin barayin hakan ya sa suka gudu cikin dajin Kwuyambana dake jihar Zamfara.”

Sanarwar ta kara da cewa sojojin ranar 14 ga watan Agusta sun kama wani hatsabibin mai garkuwa da mutane a kauyen Sambuwa mai suna,Yinusa Sulaiman da ya kware wajen tattauna biyan kudin fansa.

Har ila yau sojojin sun samu nasarar gano bindigogi da dama a wurin da aka yi artabun.
[ad_2]

More News

Ƴanbindiga sun kashe mataimakin shugaban jami’ar UDUS

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe mataimakin shugaban jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Yusuf Sa’idu.Jami’ar wadda ta bayyana rasuwar...

NDLEA ta kama tan 761,000 na miyagun kwayoyi cikin shekaru 3

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Buba Marwa, ya ce hukumar ta kama tan 761,000 na haramtattun kwayoyi...

An saka jirage uku na  shugaban ƙasa a kasuwa

Gwamnatin Najeriya ta saka jiragen shugaban ƙasa guda uku a kasuwa a wani yunkuri da mahukunta suka bayyana da cewa zai rage yawan kuɗaɗen...

Ƴan bindiga sun kashe mai POS a Ekiti

Wasu ƴan bindiga sun kashe wani mai sana'ar POS a garin Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti. Mai sana'ar ta POS dake da suna Alfa Taofeek...