
Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun kama Hauwa Abdulaziz wata mata mai shekaru 65 wacce ake zargi da yiwa mayakan Boko Haram safarar miyagun kwayoyi a jihar Borno.
An kama matar ne a ranar Juma’a a karamar hukumar Askira Uba ta jihar.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, Sani Uba jami’in yaɗa labarai na rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai dake aikin samar da tsaro arewa maso gabas ya ce anyi ittifaƙin matar na ɗaya daga cikin waɗanda suke samarwa da yan ta’adda miyagun kwayoyi a garuruwan in Askira Uba, Rumirgo, Gwahi, Wamdiyo, Uvu, da kuma Gaya.
Uba ya ce matar ta dauko ganyen tabar wiwi ne da ta samo daga jihar Taraba inda za ta kai garuruwa da dama a jihar Borno.
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa matar ta samo ganyen tabar wiwi din ne daga karamar hukumar Sarti a jihar Taraba inda ta daukota ta hanyar da suka saba bi da ita domin rarrabawa,”a cewar sanarwar.
A lokacin binciken an gano curin ganyen tabar wiwi guda 14 dake da nauyin kilogiram 30 a tare da ita.

