
Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kama wasu mutane biyu dake da hannu a tashin bom din da ya kashe mutane 5 tare da jikkata wasu 32 bayan da wani dan kumar bakin wake ya tayar da bom din dake jikinsa a wani masallaci dake kasuwar Gamboru a Maiduguri jihar Borno.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan tafkin Chadi harin bom din na haÉ—in gwiwa a tsakanin kungiyoyin yan ta’adda na the Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS), Ansaru, da kuma Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM).
Makama ya jiwo daga jami’an tsaro na sirri cewa tawagar Boko Haram karkashin jagorancin Munzir Abu Ziyadah wanda ya yi kaurin suna wajen iya hada bom shi ake zargi da hada bom na daurawa a jiki kusan 10 daga sansanin Ali Ngulde dake jihar.
Yan ta’addar sun biyo ta tsaunukan Ngoshe ya zuwa Gazuwa da Ngom inda suka watsu unguwanni daban-daban gabanin kai harin da suka shirya.
Harin Masallacin na jajiberin Kirsimeti na daga cikin wanda aka samu nasarar kaiwa.
Makama ya ce dakarun rundunar Operation Hadin ne suka kama É—aya daga cikin mutanen a ranar Litinin a garin Banki dake jihar Borno a yayin da mutum na biyu aka kama shi a Damaturu babban birnin jihar Yobe.
Ya kara da cewa É—aya daga cikin mutanen da aka kama a Borno an same shi da hadadden bom guda É—aya.

