Sojoji sun kama jirgin ruwa dauke da mai na sata a Fatakwal

Rundunar tsaron haÉ—in gwiwa ta Operation Delta Safe ta ce ta kama wani jirgin ruwa mai suna MV Ofuoma da ma’aikatansa 10 dake dakon haramtacce tataccen man fetur a jihar Rivers.

John Siyanbade kwamandan wani bangare na rundunar ya ce jirgin ruwan sojan Najeriya mai suna Pathfinder shi ne ya kama MV Ofuoma a ranar 15 ga watan Agusta a tashar jirgin ruwa ta Abuoma dake Fatakwal.

Da yake magana a wurin a madadin Riya Admiral Olusegun Ferreira, Siyanbade ya ce ana amfani da jirgin ne wajen ajiye man fetur din da aka tace ta haramtacciyar hanya.

“Ana zubawa jirgin mai da ake zargin na Diesel ne daga wani karamin jirgin katako dake kusa da jirgin” ya ce.

A daidai lokacin da aka kama jirgin ya dibi kusan lita 20, 000 daga karamin jirgin kusan jumullar lita 35000 aka samu.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...