Sojoji sun kama ɓarayin mai 43 a yankin Neja Delta

Dakarun rundunar sojan Najeriya na shiya ta 6 sun samu nasara kama mutane 43 da ake zargin suna da hannu a gudanar da wasu haramtattun matatun man fetur a yankin Neja Delta.

Danjuma Danjuma mai riƙon muƙamin mataimakin daraktan hulɗa da ƴan jaridu na rundunar ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal babban birnin jihar Rivers.

Danjuma ya bayyana cewa an kama mutanen a tsakanin ranakun 31 ga watan Maris ya zuwa  06 ga watan Afrilu a jihohin Beyalsa Delta da kuma Ribas.

Ya ƙara da cewa sojojin sun lalata haramtattun matatun mai 14 kwace jiragen ruwa 14 da kuma kwace lita 254,000 na  nau’ikan manfetur iri-iri da aka sata.

Fasa bututun mai tare dan satar mai abu ne da ya zama ruwan dare a yankin Neja Delta dake da dimbin arzikin duk da irin wannan kamen da jami’an tsaro suke yi za a iya cewa hukumomin sun gaza wajen kawo ƙarshen lamarin.

More from this stream

Recomended