Sojoji sun kama ɓarayin ɗanyen man fetur 35 a Neja Delta

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun kama mutane 35 da ake zarginsu da gudanar da haramtattun matatun man fetur da kuma lalata bututun mai a jihohi huɗu dake yankin Neja Delta.

A wata sanarwa ranar Lahadi mai riƙon muƙamin mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar sojan, Danjuma Danjuma ya bayyana jihohin Akwai Ibom, Ribas, Delta da kuma Bayelsa a matsayin inda lamarin ya faru.

Danjuma ya ce sojojin sun lalata haramtattun matatun 58 tare da ƙwace lita 11,200 na ɗanyen man fetur da aka sata da kuma lita 355,000 ta man diesel.

Ya ce an kai samamen ne daga ranar 21 zuwa 27 ga watan Oktoba  a wani ɓangare na cigaba da ƙoƙarin da rundunar take yi a yaƙi satar mai a yankin Neja Delta.

Ya ƙara da cewa a jihar Ribas sun samu nasarar lalata haramtattun matatun guda  22 a yayin da suka lalata guda 34 a jihar Akwa Ibom sai kuma jihar Bayelsa inda suka lalata guda biyu.

More from this stream

Recomended