Sojoji sun kama ƴan bindiga biyu da suka je asibiti a duba lafiyar su

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kama wasu ƴan bindiga biyu dai-dai lokacin da suka je asibiti domin a duba lafiyar su a wani asibiti dake Kaduna

Mutanen biyu sun je wani asibiti ne mai zaman kansa domin samun kulawar likitoci biyo bayan raunukan da suka samu a yayin da ake musayar wuta a wata fafatawa da jami’an tsaro.

Bisa dogaro da bayanan sirri da jami’an tsaron suka samu ne ta kai ga damƙe mutanen a wani samame da aka kai asibitin.

More from this stream

Recomended