Sojoji sun ‘halaka ‘yan fashi 135’ a Katsina da Zamfara

Sojojin Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Army

Image caption

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta lalata sansanoninsu da dama

Dakarun rundunar Hadarin Daji ta sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ‘yan fashi 135 a wani hari ta sama a jihohin Kastina da Zamfara cikin kwana biyu.

A wata sanarwa da jami’in tattara bayanai na hedikwatar tsaro da ke Abuja, Manjo Janar John Enenche, ya fitar ranar Asabar ta ce an kai hare-haren ne a ranakun Laraba 20 ga watan Mayu zuwa Juma’a 22, inda ta lalata sansanoninsu.

Daga cikin sansanonin da aka hara akwai Sansanin Abu Radde na ɗaya da na biyu, da kuma Dunya da ke ƙananan hukumomin Jibya da Ɗan Musa dukansu a Jihar Katsina, a cewar rundunar.

Sauran sun haɗa da Sansanin Hassan Tagwaye da Sansanin Maikomi da ke ƙananan hukumomin Birnin Magaji da kuma Zurmi na Jihar Zamfara.

Wannan nasara da rundunar ta yi ikirari na zuwa ne mako ɗaya bayan umarnin da Shugaba Muhammadu ya bayar na kakkaɓe ‘yan fashi daga jihohin na Katsina – jihar da ya fito – da kuma Zamfara.

Kungiya mai bincike kan tashe-tashen hankula a ƙasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutum fiye da 8,000 a rikicin arewa maso yammacin ƙasar cikin shekara 10.

Kungiyar ta ce rikicin ya raba fiye da dubu ɗari 200 da muhallansu a rikice-rikice da kuma hare-hare a yankin.

A baya-bayan nan rundunar ta sha ikirarin samun nasara a kan ‘yan bindiga, sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da take tabbatar da rahotannin.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...