Sojoji sun gano tarin bindigogi a jihar Taraba

Dakarun sojan Najeriya na rundunar samar da tsaro ta Operation Whirl Stroke sun gano tarin makamai a yayin wani farmaki a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Rundunar sojan Najeriya ta ce an kai farmakin ne a ranar 04 ga watan Janairu bayan wani bayanan sirri da suka samu kan wani mukasancin, John Ngata wanda gawurtaccen mai aikata laifuka ne a jihar.

A cewar wata sanarwa da Ahmad Zubairu mai rikon muÆ™amin jami’in hulda da jama’a na rundunar ya fitar ta ce bayan samun bayanan sojojin sun kafa wani shingen bincike ne akan hanyar Zaki-Biam inda aka kama wanda ake zargin ba tare da turjiya ba.

Bayan gudanar da bincike tare da tambayoyi wanda ake zargin ya jagoranci dakarun sojan ya zuwa wata maboyar makamai dake kauyen Amadu a karamar hukumar Takum.

Bindigogi kirar AK-47 guda 13 da harsashi 690 da kuma nakiyoyi guda 4 aka gano a maboyar makaman.

More from this stream

Recomended