Sojoji sun gano makamai a maboyar wani dan bindiga a jihar Benue

Dakarun shiya ta daya na rundunar samar da tsaro ta Operation Whirl Stroke(OPWS) sun kai farmaki wata maboyar yan bindiga dake yankin Aterange a karamar hukumar Ukum ta jihar.

Rundunar ta OPWS an samar da ita ne domin yaki da yan bindiga a jihohin Nasarawa, Benue da kuma jihar Taraba.

An kai farmakin ne da tsakar daren ranar Talata karkashin jagorancin M Babalola dake jagorantar  karamar shiyar rundunar ta 1A biyo bayan bayanan sirrin da suka samu kan maboyar wani gawurtaccen  dan bindiga da ake kira da Full Fire.

Dakarun sojan sun yi arangama da gungun yan bindigar da misalin karfe 03:45 na tsakar daren ranar Litinin. Duk da cewa gawurtaccen dan bindigar ya samu nasarar tserewa dakarun  sun kashe daya daga cikin mutanen sa a yayin musayar wuta.

Har ila yau dakarun sojan sun gano bindiga kirar AK-47 guda biyu, gidan zuba harsashi guda biyar, harsashi 163, radiyo oba oba guda biyu da kuma babur na hawa

More from this stream

Recomended