
Dakarun rundunar sojan Najeriya su samu nasarar dakile wani harin mayakan kungiyar yan ta’adda ta ISWAP da su ka kai kan wani sansanin soja dake Mairari a jihar Borno.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro ya bayyana cewa an kashe yan ta’addar da dama a yayin farmakinkamar yadda wata majiya ta bayyana masa a yayin da wasu suka jikkata.
Har ila yau sojojin sun samu nasarar tayar da bom da aka daura a jikin wasu motoci abin da ya jawo lalacewar wani sashe na titin da aka tayar da bom din.
Har ila yau sojojin sun gani baburan hawa da kuma bindigogi na yan ta’addar da suka tsere suka ka bari.

