Sojoji sun daƙile hari akan ayarin motocin Zulum

Dakarun soja dake aiki da ayarin motocin gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum sun daƙile wani farmaki da mayaƙan Boko Haram suka  kai kan jerin ayarin gwamnan akan hanyar Buni-Gari zuwa Buni-Yadi.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya rawaito cewa an kashe ƴan ta’addan da ba a san adadinsu ba a lokacin musayar wuta a yayin da aka ceto wasu matafiya bakwai daga hannun ƴan ta’addan.

Wata majiyar jami’an tsaron sirri ta bayyana cewa ayarin jerin gwanon motocin da ta ƙunshi sojoji rundunar Operation Hadin Kai,  ƴan sanda da kuma wasu jami’an gwamnatin jihar na hanyarsu ne ta dawowa daga ƙaramar hukumar Biu lokacin da ƴan ta’addar suka yi ƙoƙarin yin garkuwa da wasu fasinjoji.

Makama ya bayyana cewa gwamnan yaje garin ne a cikin jirgi mai saukar ungulu kuma baya tare da ayarin motocin lokacin da aka kai harin.

Ya ƙara da cewa dakarun sojan sun gano baburan hawa da makamai  bayan sun daƙile harin.

More from this stream

Recomended