
Dakarun shiya ta 2 na rundunar Operation Enduring Peace (OPEP) sun samu nasarar ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Kanam dake jihar Filato.
Har ila yau dakarun sun yi nasarar kashe mutane biyu masu garkuwar.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro ya bayyana cewa an kaddamar da harin kubutar da mutanen ne bayan da dakarun su ka samu labarin garkuwa da wasu mutane biyu akan titin Wanka zuwa Dengi dake karamar hukumar ta Kanam.
A cewar wata majiya dakarun sojan sun bi sawun ɗaya daga cikin yan uwan mutanen wanda masu garkuwar suka bukaci ya kai kuɗin fansa ya zuwa Dajin Madam inda anan ne aka yi musayar wutar da ta kai ga kisan masu garkuwar su biyu.
Mutane biyun da aka ceto sun hada da Muhammad Sani mai shekaru 26 da kuma Ibrahim Mamman mai shekaru 27.
Abubuwan da aka samu a hannun masu garkuwar sun hada da kuɗi dubu ₦289,000, harsashi, bindigogi da kuma wayar hannu.
Tuni dai aka mika mutanen ga iyalansu.

