Dakarun rundunar sojan Najeriya da suka fito daga Birged ta 63 a jihar Delta sun samu nasarar ceto wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su.
Dakarun sun kuɓutar da mutanen ne a wani farmaki da suka kai kan maɓoyar masu garkuwa da mutanen dake dajin Ugbolu a jihar Delta biyo bayan gamsassun bayanan sirri da suka samu kan ayyukan ɓatagarin.
Wani saƙo da rundunar sojan Najeriya ta wallafa a shafin Facebook ya ce an ceto mutanen ne a ranar Litinin 9 ga watan Disamba bayan da aka yi musayar wuta da Waɗanda suka yi garkuwa da su.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun shafe kwanaki a cikin dajin a tsare a ya yin da masu garkuwa da su ke ƙoƙarin ganin an biya su kuɗin fansa kafin su sake su.
Sanarwar ta ce an kai mutanen asibiti likotoci su duba lafiyar su a kafin daga bisani ka miƙa su ga iyalansu.