9.7 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeMoreSojoji sun cafke mai yiwa mayakan Boko Haram tsegumi a kan ayyukansu

Sojoji sun cafke mai yiwa mayakan Boko Haram tsegumi a kan ayyukansu

Date:

Related stories

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Tinubu ya bada umarnin sakin yaran da aka gurfanar a gaban kotu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin ...
spot_imgspot_img
BH

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da ke aiki karkashin Operation Lafiya Dole sun cafke wani da ake zargin yana yiwa Boko Haram leken asiri a kan sojojin ƙasar.

Ayyukan leken asirin mutumin da aka cafke da abokan aikinsa nada nasaba da harin da ƴan ta’addan suka kai wa sojoji a yankin Kamuya na jihar.

A wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar sojin Birgidiya janar Mohammed Yerima ya bayyana sunan mutumin da ‘Modu Ari’.

Sanarwar ta kuma ce mutumin da ake zargin ya amsa cewa shi ne yake tseguntawa mayakan Boko-Haram yadda sojoji ke gudanar da ayyukansu da kuma wurin da suke.

“Har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano yadda masu ba da labaran cikin gida wadanda aikinsu ya jefa rayuwar sojoji cikin hadari a kan iyakokin yankin Timbuktu Triangle, “in ji kakakin.

A kwamakin da suka gabata ne mayakan Boko Haram suka kai harin kwantar-ɓauna a kan sojoji da ke sintiri a yankin Kamuya .

Sai dai sojojin sun yi ikikarin daƙile harin amma ba su bayyana adadin wadanda suka jikkata ko rasa rayukansu.

Matsalolin tsaro a Najeriya na sake rincaɓewa musamman a yankunan arewa maso gabashin ƙasar, yanayin da ya tilastawa Majalisar Dinkin Duniya dakatar da ayyukanta a wasu yankunan Borno saboda ɓarnar da Boko Haram ke yi wa harkokin ba da agaji.

Ko a maraicen Lahadin sai da wasu da ake zargin ‘yan Boko Hasram ne sun sake kai farmaki a Dikwa.

Hare-haren baya-bayan nan a Damasak sun yi sanadin tserewar dubban mutane daga garin, waɗanda akasari suka tsallaka Jamhuriyar Nijar gudun hijira.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here