Sojoji 20 sun rasa rayukansu a jihar Borno

Dakarun sojan Najeriya aƙalla 20 aka kashe a wani hari da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP da kaiwa akan sansaninsu.

Ƴan ta’addan sun farma sansanin sojan dake garin Mallam Fatori a jihar Borno a ranar Juma’a inda wani soja da ya tsira da ransa ya fadi cewa sun ɗauki tsawon sama da sa’o’i uku suna artabu.

Boko Haram da kuma ISWAP sun ɗauki tsawon lokaci suna kai farmaki kan jami’an tsaro da  fararen hula a yankin arewa maso gabashin Najeriya inda suka kashe dubban mutane tare da raba wasu da muhallin su.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters babban kwamandan soja na daga cikin dakarun da aka kashe kamar yadda majiyar jami’an tsaron ta bayyana.

“Sun yi mana ruwan harsashi ta ko’ina,” ɗaya daga cikin sojojin ya faɗawa Reuters ta wayar tarho ya ƙara da cewa shammatarsu aka yi.

Wasu mutane da suka tsere daga garin mai iyaka da Nijar sun ce har ya zuwa ranar Asabar da daddare anga wasu daga cikin maharan a Mallam-Fatori.

Malakaka Bukar wani mamba a Civilian JTF ya ce maharan sun ƙona wasu gidaje a garin.

More from this stream

Recomended