Wasu sojojin da suka yi ritaya sun gudanar da zanga-zanga a ƙofar shiga ma’aikatar kuɗi dake Abuja kan wasu hakkokinsu da ba a biya su ba.
Rukunin ƴan fanshon sun tare kofar shiga ma’aikatar da kujeru da rumfuna tare da rataye alluna dake ɗauke da rubutun dake kira a gaggauta biyan su hakkinsu da ba a biya su ba.
Zanga-zangar na zuwa ne ɗan lokaci kadan da suka gudanar da makamanciyar irinta a cikin watan Disamba lokacin da ƴan fanshon suka tsayar da ayyuka a ma’aikatar kan gazawar gwamnati na biyansu hakkokinsu na su.
Biyo bayan zanga-zangar ta watan Disamba gwamnatin tarayya ta biya kaso 50 na hakkinsu da ya rage inda tayi alkawarin biyan abun da ya yi saura.
Yan fanshon sun ce har yanzu gwamnatin ta gaza cika alkawarin.