Sojin saman Najeriya na ci gaba da fatattakar ‘ƴan bindigar Zamfara

Tun bayan da shugaban kasa Muhammad Buhari ya bawar rundunar sojan Najeriya damar yin duk abinda ya dace wajen fatattakar barayin da suka addabi jihar Zamfara.yanzu za a iya cewa haka ya fara cimma ruwa.

Mallam Ibrahim Janyau, dake zama shugaban wata kungiyar samar da zaman lafiya a Zamfara, ya nuna gamsuwarsu da aikin da sojojin saman kasar ke yi a yankunansu. Ya kuma bayar da missali da garin Munaka dake gundunar Mada, inda wani jirgin yaki yayi shawagi a yankin, inda hakan yasa ‘yan bindigar suka gudu cikin karkara.

Sai dai kuma yayin da sojojin ke ci gaba da murkushe ‘yan bindigar, ana ci gaba da samun kwarar ‘yan gudun hijira zuwa Katsina mai makwabtaka da jihar ta Zamfara.

Majiyoyi daban-daban sun tabbatarwa da Muryar Amurka cewa gwamnatin Katsina na taimakawa ‘yan gudun hijirar, kamar yadda shima gwamnnan Katsina Aminu Bello Masari, ya tabbatarwa da wakilin Muryar Amurka.

Gwamna Masari, ya tabbatar da cewa da kansa ya ziyarci wajen da ‘yan gudun hijirar suke, domin gano hanyar da zasu ‘kara taimakawa ‘yan gudun hijirar.

More News

Ƴan sanda sun kama masu sayen kuri’a a zaben gwamnan Edo

Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya sun kama wasu mutane 9 da ake zarginsu da sayen kuri'a da kuma mallakar kuri'ar da aka riga aka...

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...