Sojan saman Najeriya sun kashe ƴan ta’adda masu yawa a jihar Neja

Rundunar sojan saman Najeriya ta kashe ƴan ta’addada dama a wani farmaki da ta kai da jiragen yaƙi a Dajin Alawa dake ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya ce hari na sojan saman an kai shi ne kan Saddiku, Umar Taraba da Kabiru Doctor jagororin kungiyar ƴan ta’adda ta Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’Awati Wal-Jihad ( JAS ) waɗanda aka kyautata zaton suna rayuwa ne a dajin.

Wasu majiyoyin jami’an tsaron sirri sun faɗawa Makama cewa harin ya lalata makamai da dama, ababen hawa, babura  ta re yiwa ƴan ta’addan mummunan ɓarna.

Makama ya ce cigaba da cewa yawan harin sojan saman ke kaiwa ya tilastawa ƴan ta’addar sauya matsuguni daga dajin ya zuwa Birnin Gwari dake jihar Kaduna.

An daɗe ana zargin kungiyar ƴan ta’addan Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’Awati Wal-Jihad (JAS) da kafa sansanin a dajin na Alawa.

More from this stream

Recomended