
Dakarun rundunar sojan Najeriya dana sojan saman Najeriya sun dakile wani hari da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP da kaiwa kan sansanin sojoji dake garin Rann a karamar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akanvyankin tafkin Chadi lamarin ya faru da safiyar ranar Laraba lokacin da yan ta’addar suka yi basaja da shiga irin ta Fulani makiyaya suka kaddamar da hari Kan sansanin.
Makama ya ce dakarun sun mayar da martani inda suka yi dauki ba dadi da maharan har zuwa lokacin da jirgin saman sojan Najeriya ya kawo musu dauki a lokacin harin.
Ya kara da cewa suna hango jirgin yan ta’addar sun yi kokarin tarwatsewa inda suka fantsama daji domin kaucewa hari ta sama.
Ya cigaba da cewa duk da haka sai da matukin jirgin yakin sojan Najeriya yabi diddigin wasu yan ta’addar da suka tsere a cikin wata Hilux inda ya kashe da yawa daga ciki tare da lalata motar.
Makama ya ce kawo yanzu ba a san yawan mutanen da aka kashe ba a bangaren yan ta’addar.