
Kungiyar shugabannin jam’iyar PDP na jihohi sun jaddada cikakken goyon bayansu da biyayyarsu ga shugabancin jam’iyar karkashin Umar Damagum inda suka yi fatali da tsagin shugabancin, Abdulrahaman Muhammad.
A wata sanarwa da aka fitar bayan taronsu a ranar Alhamis kungiyar da ta ƙunshi shugabannin jam’iyar na jihohi 29 ta ce Damagum shi ne halastaccen shugaban jam’iyar PDP kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada
Kungiyar ta nesanta kanta da shugabancin , Abdulrahaman.
Har ila yau kungiyar ta yabawa irin hadin kan da ake samu a tsakanin shugabancin jam’iyar na kasa da kuma kungiyar gwamnonin jam’iyar PDP karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad da kuma kwamitin amintattun jam’iyar karkashin jagorancin, Adolphus Wabara.
Kungiyar ta kuma yi kira ga reshenta na jihohi da su dauki matakin ladabtarwa kan duk wani dan jam’iyar dake neman tayar da zaune tsaye.

