Shugabannin kasashen duniya sun halarci binne Kofi Annan


An gudanar da kasaitaccen biki wajen binne Mista Kofi Annan.

Shugabannin kasashen duniya sun mika sakonnin yabo ga marigayi Kofi Annan, daya daga cikin ‘yan Afirka da suka shahara, a lokacin binne shi da aka yi a kasarsa ta Ghana.

Wannan ne karshen kwanaki uku na zaman makoki da gwamnatin kasar ta ayyana, kuma dubban ‘yan kasar sun ziyarci babban dakin taro na birnin Accra inda aka ajiye gawarsa domin nuna jimaminsu.

Mista Annan ya mutu a ranar 18 ga watan Agusta yana da shekara 80 da haihuwa.

Ghana Launin ja da baki sune masu zaman makoki suka fi sakawa a lokacin zaman makoki a Ghana.

Ghana Launin ja da baki sune masu zaman makoki suka fi sakawa a lokacin zaman makoki a Ghana.

Ya zama babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya daga 1997 zuwa 2006, kuma shi ne bakar fata na farko da ya taba rike wannan babban mukamin na diflomasiyya.

An kuma ba shi lambar yabo ta Nobel a 2001 saboda rawar da ya taka ta inganta ayyukan majalisar, a lokacin da ake yakin Iraki da ake kuma fama da annobar cutar AIDS ko SIDA.

An ajiye gawar Mista Annan a wani dakin taro bayan da ta isa Ghana daga Switzerland.

An ajiye gawar Mista Annan a wani dakin taro bayan da ta isa Ghana daga Switzerland.

A wajen bikin, babban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya mai ci, Antonio Guterres ya ce Mista Annan ya kasance mutumin da ya mayar da majalisar ta zama mai taimaka wa wajen rage fitunu a duniya.

Wani kwararren mai zane ya rika zana hotunan Mista Annan tun bayan mutuwarsa.

Wani kwararren mai zane ya rika zana hotunan Mista Annan tun bayan mutuwarsa.

Wadanda suka halarci bikin sun sanya kaya masu launin baki da ja, kuma sun cika babban dakin taro na Accra mai daukan mutum 4,000.

Wasu kuma sun kalli bikin ne a wasu manyan allunan talabijin da aka kafa musamman domin nuna wa jama’a kai tsaye yadda al’amura ke gudana.

Kojo Amoo-Gottfried wanda dan dan uwan Mista Kofi Annan ne, ya karanta sakon karrama wa a lokacin bikin, inda ya bayyana cewa Mista Annan ya yi jagorancin boren kin cin abinci a lokacin yana dan makaranta domin yadda ake ba wa ‘yan makaranta abinci maras kyau.

An rika kada ganguna a wurin jana'izar domin tunawa da ayyukan da Mista Annan ya gudanar a lokacin rayuwarsa.
An rika kada ganguna a wurin jana’izar domin tunawa da ayyukan da Mista Annan ya gudanar a lokacin rayuwarsa.

Tshuwar sarauniyar kasar Holland Gimniya Beatrix na daga cikin wadanda suka halarci zaman makokin tare da matar danta Gimbiya Mabel. Dukkansu aminan Mista Annan ne.

Sarkin Asante Otumfuo Nana Osei Tutu II, ya nada wa Mista Annan sarautar “Busumuru” a 2012 domin karrama ayyukan da ya yi na diflomasiyya a duniya.

Basumuru sunan daya daga cikin takubban da ke makale a karagar zinare ta masarautar Asante.

Sarakunan gargajiya na Ghana sun halarci bikin tare da wasu manyan lemomi na musamman.
Sarakunan gargajiya na Ghana sun halarci bikin tare da wasu manyan lemomi na musamman.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya bayyana Mista Annan a matsayin “daya daga cikin shararrun mutanen wannan karnin da muke ciki”.

Al'umomin Ghana na alfahari da ayyukan da Mista Annan yayi a lokacin rayuwarsa.

Al’umomin Ghana na alfahari da ayyukan da Mista Annan yayi a lokacin rayuwarsa.

Babban limamin cocin Anglika na Kumasi, wanda shi ne asalin garin da Mista Annan ya fito, Rabran Daniel Sarfo ya ce: “Yau rana ce da aka kafa tarihi a nan Ghana. Daya daga cikin shahararrun ‘ya’yanmu ne ke kwance a nan.”

Amma muna matukar farin ciki cewa ubangiji ya yi amfani da shi wajen gudanar da ayyukan da suka inganta rayuwar dan Adam, da samar da zaman lafiya. A yau aikinsa ya kammala.”

Dukkan hotunan nan na da hakkin mallaka akansu.

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...