Shugabannin jam’iyar PDP sun gana da Goodluck Jonathan

Shugabannin jam’iyar PDP na kasa a karkashin jagorancin, Kabiru Tanimu Turaki sun gana da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a babban birnin tarayya Abuja.

Taron ganawar ya gudana ne a ofishin tsohon shugaban kasar dake unguwar Maitama.

Babu wata sanarwa da aka fitar kawo yanzu kan dalilin ganawar  amma wasu kafafen yada labarai ganin bata rasa nasaba da halin da jam’iyar take ciki da kuma siyasar Najeriya baki É—aya.

A watan Nuwamba ne wani tsagi na jam’iyar ta PDP dake samun goyon bayan, Bala Muhammad gwamnan jihar Bauchi da kuma Seyi Makinde na jihar Ondo suka gudanar da babban taron jam’iyyar a Ibadan babban birnin jihar Oyo inda aka zabi Tanimu Turaki a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

More from this stream

Recomended