
Tsagin jam’iyar PDP dake samun goyon bayan tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya kira wani taron gaggawa na shugabannin jam’iyar da kuma kwamitin amintattun jam’iyar ta PDP.
Abdulrahaman Muhammad shugaban PDP na tsagin shi ne ya kira taron da zai gudana a hedkwatar jam’iyar dake Wadata Plaza a birnin tarayya.
Tuni dai tsagin jam’iyar na PDP da sabon shugaban jam’iyyar, Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta ya sanar da korar Wike da kuma mutanen dake masa biyayya a wurin taron zaben shugabanni da jam’iyar ta gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Tsohon sakataren jam’iyar ta PDP kuma makusanci ga Wike shi ne ya sanya hannu a takardar da ta kira taron.

