Shugaban Koriya Ta Arewa ya bayyana ƴarsa ga duniya a karon farko

Asalin hoton, Getty Images

A karon farko Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana ƴarsa ga duniya, inda ya tabbatar da jita-jitar da ake yaɗawa a kan cewa yana da ƴa mace.

Ƴar wadda aka ce sunanta Kim Chu-ae ta raka shi ziyartar harba wani makami mai linzami a ranar Juma’a.

Dukansu biyu sun tsaya kusa da juna a lokacin harba makamin, wanda Amurka ta yi Allah-wadai da harba shi.

Mista Kim na jagorantar ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya sirri kuma ba a san abubuwa da dama ba game da rayuwarsa.

Akwai hotuna da dama da kafar watsa labarai ta Koriya ta Arewa ta wallafa waɗanda ke nuna uba da ƴar tasa suna riƙe da hannun juna, haka kuma suna magana da jami’ai.

Bayyanar ƴar Kim Jong Un ya zama muhimmin abin tattaunawa matuƙa musamman ga masu sharhi inda wannan labarin ma a wurinsu ya wuce labarin harba makami mai linzami.

Makami mai linzamin kuma irin mai tafiya daga wata nahiya zuwa wata nahiya ne kuma yana da ƙarfin zuwa har ƙasar Amurka.

Amma me yasa ake ganin bayyanar ƴarsa na da muhimmanci? Na farko saboda hakan na nuni ga makomar shugabanci da shirin nukiliya na ƙasar.

Haka kuma wannan lamari yana saka ayar tambaya ga abubuwa kamar shin hakan na nufin za ta zama wadda za ta gaji Mista Kim inda wata rana za ta jagoranci Koriya ta Arewa?

Ana kyautata zaton Mista Kim ɗin zai so ƴar tasa ta gaje shi.

Tambaya ta biyu ita ce me ya sa sai yanzu zai nuna wa duniya ita? Har yanzu yarinya ce.

Idan yana shirin barinta ne ta karɓi ragamar shugabancin? shin hakan na nufin shugaban mai shekara 38 na fama da wata rashin lafiya?

Lafiyar shugaban ita ce abar da aka fi tattaunawa a kanta sakamakon a halin yanzu ita ce za ta iya zama wata cikas ga mulkinsa.

Haka kuma me hakan ke nufi ga shirin nukiliya na Koriya?

Bayyana ta a irin wannan lokaci mai muhimmanci na ƙara nuni da cewa watakila wata rana za ta taka wata muhimmiyar rawa wurin samar da makamai a ƙasar.

A ƴan kwanakin nan Mista Kim ya bayyana cewa ba zai taɓa bayar da makaman nukiliyansa ba.

Wannan wata hanya ce da yake nuna cewa makamansa na nukiliya za su ci gaba da kasancewa har abada.

Asalin hoton, KCNA via Reuters

Michael Madden, wanda wani ƙwararre ne daga Koriya Ta Arewa da ke Washington ya bayyana cewa yana kyautata zaton Chu-ae na da shekara 12 zuwa 13.

Ya bayyana cewa nuna ta da ya yi ga duniya watakila wata alama ce da ke nuna cewa Mista Kim na nuna wa duniya cewa wadda za ta gaje shi daga jininsa za ta fito.

A watan Satumba, akwai masana a ƙasar da dama da suka bayar da labarin cewa an nuno Chu-ae a wani bidiyo na zagayowar samun ƴancin ƙasar.

Sai dai wannan duk jita-jita ce haka kuma hukumomi a ƙasar ba su tabbatar da hakan ba.

More News

Ƴan bindiga sun buɗe wuta kan motar kulob ɗin Sunshine Stars

Ƴan wasa da kuma jagororin kungiya ne suka jikkata a wani hari da ƴan bindiga suka kai kan tawagar kungiyar kwallon kafa ta Sunshine...

Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 5 tare da lalata sansaninsu 4 a Borno

Sojojin rundunar kasa da kasa dake samar da tsaro a yankin tafkin Chadi sun kashe mayaƙa 6 na ƙungiyar ƴan ta'adda ta ISWAP...

Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje da Ta’aziyya Jihar Kaduna

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kai ziyarar jaje da ta'aziyya jihar Kaduna na mutanen da harin jirgin sojoji ya kashe a ƙauyen Tudun...

Tudun Biri:An gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya

Masu zanga-zanga a ranar Laraba sun tsinkayi ginin majalisar dokokin tarayya dake Abuja kan kisan da jirgin sojoji ya yiwa fararen hula a Kaduna...