Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga wani taron sirri na gaggawa da manyan hafsoshin tsaro a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Talata.
Taron ya gudana ne kasa da sa’o’i 24 bayan Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya yi murabus daga mukaminsa.
Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede ne ya jagoranci tawagar tsaron.
Sauran manyan hafsoshin da suka halarta sun haɗa da Shugaban Hafsoshin Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar W. Shaibu; Shugaban Hafsoshin Sojojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke; da Shugaban Rundunar Sojin Ruwa, Vice Admiral I. Abbas.
Haka kuma, Shugaban Hukumar Binciken Tsaro ta Ƙasa (CDI), Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye, Darakta Janar na DSS, Adeola Ajayi, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, duk suna cikin taron.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro ke ƙara ta’azzara a sassan ƙasar. Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan abubuwan da aka tattauna ba.
A baya dai, Shugaba Tinubu ya sanar da nadin tsohon Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Christopher Musa, domin maye gurbin Badaru a matsayin sabon Ministan Tsaro.

