Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sarkin Musulmi A Fadar Shugaban Ƙasa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a ranar Juma’a, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani, Dada Olusegun, ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na X (tsohon Twitter).

Ganawar ta zo ne ‘yan kwanaki bayan Tinubu ya gana da shugaban darikar Katolika na Abuja, Bishop Ignatius Ayau Kaigama.

Olusegun ya bayyana cewa ganawar tana cikin shirin tattaunawar da shugaban ƙasa yake yi da shugabannin addini da na gargajiya a fadin ƙasar.

A cewarsa: “A cikin jerin tattaunawa da shugabannin addini da na gargajiya, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi, Mai Alfarma, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, a Fadar Shugaban Ƙasa yau, ‘yan kwanaki bayan ganawarsa da Bishop Ignatius Ayau Kaigama, shugaban cocin Katolika na Abuja.”

Ana sa ran irin waɗannan ganawa za su taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban a Najeriya.

More from this stream

Recomended