Shugaba Tinubu ya Dakatar da Ministar Jinƙai, Betta Eddu Saboda Zargin Baɗakalar Kudi

Rahotanni da ke fitowa daga fadar shugaban kasa na nuna cewa Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar ji kai saboda zargin badakalar kudi.

An bayyana dakatarwar ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale, ya rattaba wa hannu a yau Litini.

Wannan dakatarwa tana da alaƙa da wasu zarge-zarge da ministar ke fuskanta na ƙoƙarin karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe ta ɓarauniyar hanya.

More from this stream

Recomended