Shin kwallo nawa Benzema ya ci wa Real Madrid kakar bana?

Karim Benzema

Karim Benzema ya ci kwallo 15 a wasa 24 da ya buga wa Real a bana ya kuma bayar da biyar aka zura a raga.

Ranar Asabar Real Madrid ta yi nasarar doke Deportivo Alaves da ci 4-1 a wasan mako na 20 a gasar La Liga.

Karim Benzema ne ya ci wa Real kwallo biyu a wasan, yayin da Casemiro da Eden Hazard suma kowanne ya zura kwallo a raga, Jose Luis Sanmartin Mato ne ya zare wa Alaves kwallo daya.

Kwallayen da Benzema ya ci a La Liga a bana:

A gasar La Liga Benzema ya ci kwallo 10, wanda ya zura daya a ragar Levente da Valencia da Eibar da kuma Granada.

Kungiyoyin da ya ci kwallo biyu a La Liga sun hada da Huesca da Athletic Bilbao da kuma Alaves.

Kwallayen da Benzema ya zura a raga a Champions League a bana:

A kakar cin kofin Zakarun Turai ta bana wato Champions League, kwallo uku Benzema ya zura a ragar Borussia Monchengladbach wadda ya ci biyu da Inter Milan da ya ci daya.

Shi ne kuma ya ci kwallo a Spanish Super Cup da Real ta yi da Athletic Bilbao.

Wasan da ya bayar da kwallo aka zura a raga a bana:

Karawa hudu ce Benzema ya bayar da da kwallo aka zura a raga.

Wasannin sun hada da wadda ya bai wa Valverde ya ci Betis da Barcelona da kuma Huesca da wasan da ya bai wa Modric da kuma Lucas Vazquez da kowanne ya ci Eibar.

More from this stream

Recomended