Shettima ya ziyarci iyalan Buhari a London

Mataimakin shugaban kasa,Kashim Shettima ya kai wa iyalan marigayi Muhammad Buhari ziyarar ta’aziya a gidan da su ke zaune a birnin London.

Shettima ya kuma gana da Mammman Daura dan uwa kuma makusancin tsohon shugaban kasar da kuma wasu daga cikin iyalan na Buhari a lokacin ziyarar ta ranar Litinin.

A ranar Lahadi ne Shettima ya tashi daga Abuja zuwa London bisa umarnin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya bashi na ya je domin tawo da gawar marigayin.

Buhari ya ra su a wani asibiti dake birnin London bayan da ya kwashe kwanaki yana jinya.

More from this stream

Recomended