Shettima Ya Tafi Davos Don Wakiltar Nijeriya A Taron Tattalin Arziƙin Duniya Na 2025

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja domin wakiltar Nijeriya a taron shekara-shekara na Tattalin Arziƙi na Duniya (WEF) na 2025, wanda za a gudanar a Davos, Switzerland.

A cewar wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, an bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasar zai haɗu da shugabannin duniya, manyan ‘yan kasuwa, da wakilan ƙasashen ci gaba domin tattauna halin da tattalin arziƙin duniya ke ciki da kuma hanyoyin da za a inganta shi.

Shettima zai halarci muhawarori da taruka daban-daban, ciki har da wani taro da Bankin Ci Gaban Afrika (AfDB) ya shirya, mai taken “Taswirar Haɗin Gwuiwar Jari Don Kasuwannin Ci gaba na Afrika.” Haka kuma, zai shiga tattaunawa kan batun “Kasuwancin Zamani a Matsayin Jigon Ci Gaba a Afrika,” don tallafa wa yarjejeniyar AfCFTA ta fannin kasuwancin zamani.

Bugu da ƙari, Mataimakin Shugaban Ƙasar zai halarci tattaunawa kan “Manyan Barazanar da Duniya Ke Fuskanta a 2025,” tare da wasu mahimman batutuwa da suka shafi tattalin arziƙi da ci gaban Afrika.

Ana sa ran Shettima zai dawo gida bayan kammala ayyukan da suka shafi taron, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

More from this stream

Recomended