Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya gayyaci shugaban kamfanin mai na NNPCL, Mele Kyari da kuma ƙaramin ministan harkokin man fetur, Henry Lokpobiri ya zuwa wani taro.
Kyari, Lokpobiri da Ugbogu Ukoha shugaban hukumar NMDPRA dake lura da tacewa da kuma rarraba man fetur a Najeriya sun halarci ganawar da ta gudana a fadar Aso Rock dake Abuja.
An gudanar da taron ne bisa umarnin da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bawa Shettima da ya shafi ƙarin kuɗin man fetur.
Mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu shima ya halarci wurin taron.
A ranar Talata ne kamfanin na NNPCL ya kara kuɗin man fetur a gidajen mansa dake faɗin Najeriya.
A yanzu dai ana sayar da man fetur ɗin akan ₦855 a gidajen mai na NNPCL dake Lagos a yayin da farashin ya haura sama da ₦900 a wasu jihohi.