Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ziyarci mutanen da suka jikkata a harin ƙunar baƙin wake da aka kai a jihar Borno.
A ranar Asabar ne wasu mata da ake zargin ƴan ƙunar baƙin wake ne suka tashi bama-bamai a ƙaramar hukumar Gwoza dake jihar.
Tuni dai aka saka dokar hana fita a garin gudun kada a ƙara kai makamancin harin.
A lokacin ziyarar da yakai Asibitin Ƙwararru na Borno, Shettima ya miƙa saƙon jajen shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ga mutanen da abun ya shafa da kuma gwamnatin jihar Borno. Ya kuma ce mutanen da suka mutu a harin sun ƙaru ya zuwa 32.
Shettima ya ce musamman shugaban ƙasar ya umarce su da su kawo ziyarar jaje da kuma ta’aziyar saboda yadda harin ya taɓa zuciyarsa sosai.
A yayin ziyarar mataimakin shugaban ƙasar na tare da shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, Ministan Sufuri da na Gona da kuma bulaliyar majalisar dattawa.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma halarci jana’izar mahaifiyar, Ali Modu Sharif tsohon gwamnan jihar Borno.